Sardaunan Gombe | Jihar Gombe, Najeriya Ɗan Takarar Gwamna Na APC 2027 English Hausa
Gwamnaga Gombe Faɗa Wa Gwamna

2027 – 2031

Manufofin Kawo Sauyi Mai Inganci

Tsarin shekaru huɗu na samar da ayyuka masu gamsarwa. Ginshiƙai bakwai, manufofi bayyanannu da bayar da bayani ga jama'a domin gina Gombe mafi girma.

Kundin Manufofin IMPACTS
Dr. Jamilu Isyaku Gwamna with Governor Muhammadu Inuwa Yahaya

Alƙawarina

Alƙawari Ga Al'ummar Jihar Gombe

Mulki ba wata alfarma ba ce, illa amana mai girma da ake samu ta hanyar hidima, a tabbatar da ita ta hanyar aiwatarwa, sannan a sabunta ta ta hanyar yin aiki cikin gaskiya da rikon amana.

Jihar Gombe a yau tana cin gajiyar gagarumin aikin jagoranci na Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, CON (Dan Majen Gombe), wanda ya shimfiɗa ingantaccen tubalin ci gaba. Ban zo domin in sake ƙirƙirar abin da aka riga aka fara ba. Na zo ne domin tabbatar da cewa ayyukan ci gaba sun ci gaba da tafiya, kuma kowa ya amfana da su.

Tsarinmu na ginshiƙai bakwai ba taken yaƙin neman zaɓe kawai ba ne. Tsari ne na aiki wanda za a iya auna nasarorinsa, mai yiwuwa a aiwatar, kuma wanda ya dogara da ainihin buƙatun al'ummarmu.

Ina gayyatar kowane ɗan Jihar Gombe da duk masu ruwa da tsaki su karanta wannan kundin, su tattauna shi, su yi tambayoyi, sannan su ba mu amanar aiwatar da shi.

Jamilu Isyaku Gwamna

Manyan Manufofin Shekaru Huɗu

Abin Da Za Mu Cim Ma Zuwa 2031

A ƙarshen wa'adin shekaru huɗu, sababbin ayyukan yi 100,000 a dukkan ɓangarori, ba tare da ƙirga aiki guda sau biyu ba, tare da rahotanni bisa kowane fanni.

100,000 Sababbin Ayyukan Yi A Dukkan Ɓangarori
10,000 Ayyukan Yi Kai Tsaye A Masana'antu
50,000 Ayyukan Yi Na Kaikaice A Masana'antu Da Sarƙar Kayayyaki
20,000 Ayyukan Yi A Fannin Kiwo Da Sarrafa Kayayyakinsa
110 Rukunan Noma
100 Ƙungiyoyin Haɗin Gwiwar Kiwo Da Madara
50,000 Ƙanana Da Matsakaitan Sana'o'i Da Za A Tallafa
3 Cibiyoyin Masana'antu Ko Sarrafa Amfanin Gona
10,000 Gidaje Masu Araha Ko Filayen Gini
2 Cibiyoyin Kiwon Lafiya Na Matakin Farko A Kowace Mazaba

Za a wallafa rahotannin auna ci gaba kowane wata uku.

Ginshiƙai Bakwai

Ginshiƙai Bakwai, Tsari Guda

Kowane ginshiƙi yana ƙunshe da alƙawura bayyanannu, manufofin da za a iya aunawa, lokutan aiwatarwa da hanyoyin bayyana sakamako ga jama'a. Taɓa harafi domin ganin bayani.

Ababen More Rayuwa Da Muhimman Ayyukan Jama'a

Kammalawa, Kulawa, Faɗaɗawa Da Gina Sababbi

Babbar Manufa

Kammala ayyukan da ake yi, kula da kadarorin da ake da su, faɗaɗa muhimman ayyukan hidima, da gina kayayyakin more rayuwa da Gombe ke buƙata.

Muhimman Alƙawura

  • Kammala dukkan ayyukan tituna, gadoji, fitilun tituna masu amfani da hasken rana da sauran ayyukan da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta fara, bisa jadawalin da aka tsara.
  • Shirin Network 11/100 2.0 zai gina ƙarin kilomita 1,000 na hanyoyi, tare da samar wa kowace al'ummar manoma hanyar mota zuwa kasuwa mafi kusa.
  • Aƙalla gidaje masu araha ko filayen gini 10,000 zuwa 2031, da gina ko gyara rijiyoyin burtsatse 50 a kowace LCDA.
  • Tashar wutar hasken rana mai ƙarfin megawatt 100 tare da masu zuba jari, bas masu amfani da lantarki a birnin Gombe da bas na CNG masu haɗa manyan garuruwa.

Masana'antu Da Bunƙasa Sarrafa Kayayyaki

Daga Gonaki Zuwa Masana'antu, Daga Gombe Zuwa Duniya

Babbar Manufa

Sauya tsarin fitar da ɗanyen albarkatu zuwa fitar da kayayyakin da aka sarrafa ko aka kammala ƙera su.

Muhimman Alƙawura

  • Kammalawa da fara aiki a Yankin Musamman na Raya Noma da Kiwo.
  • Mataki na biyu na Filin Masana'antu na Muhammadu Buhari, a matsayin ɗaya daga cikin rukunan masana'antu guda uku.
  • LCDA ɗaya, samfuri ɗaya: fitaccen samfuri ga kowace LCDA, tare da wuraren sarrafawa, tallafin kuɗi da damar kasuwa.
  • Ayyukan yi kai tsaye 10,000 da na kaikaice 50,000 a masana'antu, tare da rahotanni kowane kwata.

Ci Gaban Jama'a Da Albarkatun Ɗan Adam

Haɓaka Ilimi, Kiwon Lafiya, Ƙwarewa Da Damar Jama'a

Babbar Manufa

Kowane yaro ya samu ilimi, kowace uwa ta samu kariya, kowane matashi ya samu ƙwarewa, kuma kowace mace ta samu damar dogaro da kai.

Muhimman Alƙawura

  • Ɗaukar sababbin malamai 1,000, horar da malamai 10,000, da mayar da yara 100,000 da ba sa makaranta cikin aji a kowace shekara.
  • Cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda biyu masu cikakken aiki a kowace mazaba, da kulawar ciki, haihuwa da bayan haihuwa kyauta.
  • Biyan kuɗin jarrabawar NECO, WAEC da JAMB ga dukkan ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare.
  • Asusun Kasuwancin Matasa mai rance mai ƙarancin ruwa, kashi 40% ga matasa da kashi 35% na naɗe-naɗe ga mata.

Noma Da Sauya Rayuwar Karkara

Ciyar Da Ƙasa Da Inganta Rayuwar Karkara

Babbar Manufa

Faɗaɗa amfani da injinan noma, ƙara yawan amfanin gona, rage asarar bayan girbi, da ƙarfafa tattalin arzikin karkara.

Muhimman Alƙawura

  • Faɗaɗa ban-ruwa a madatsun Dadin Kowa, Balanga da Cham, da tallafin kayan noma ga manoman rani.
  • Aƙalla rukunan noma 110 a dukkan ƙananan hukumomi 11, da ƙara amfanin manyan gonaki da aƙalla kashi 25%.
  • Jami'an faɗakarwa na noma 300, da gonar gwaji da cibiyar injinan noma a kowace LCDA.
  • Ma'aikatar Raya Kiwo, ƙungiyoyin madara 100, da majalisun sulhun manoma da makiyaya.

Kasuwanci, Ciniki Da Yawon Buɗe Ido

Tallafa Wa 'Yan Kasuwa, Mata Da Matasa

Babbar Manufa

Ƙarfafa ƙananan kasuwanci, faɗaɗa cinikayya, da mayar da Gombe babbar cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya bayan Kano.

Muhimman Alƙawura

  • Asusun Tallafin 'Yan Kasuwa tare da Bank of Industry da SMEDAN ga ƙananan 'yan kasuwa, matan kasuwa da masu ƙananan sana'o'i.
  • Zamanantar da Babbar Kasuwar Gombe, Tsohuwar Kasuwa, Kasuwar Tike da kasuwar zamani a kowace shiyyar sanata.
  • Rijistar kasuwanci cikin sa'o'i 48: fom guda, ofishi guda da jadawalin kuɗi guda.
  • Madatsar Dadin Kowa da tsaunukan Tula a matsayin manyan wuraren yawon buɗe ido, da baƙi 250,000 a kowace shekara zuwa 2031.

Fasahar Zamani Da Damar Dijital Ga Kowa

Kai Gombe Zuwa Mataki Mai Girma A Fasahar Zamani

Babbar Manufa

Gombe da ba ta rungumi fasahar dijital ba za ta kasance a baya.

Muhimman Alƙawura

  • Intanet mai sauri a kowace LCDA, da Wi-Fi kyauta a wuraren shakatawa, kasuwanni, tashoshin mota da asibitoci.
  • G-ODA: horar da aƙalla matasa 150,000 a ƙwarewar dijital da ke kaiwa ga ayyukan yi zuwa 2031.
  • Babbar tashar intanet guda domin neman hidimomin gwamnati, bibiyar buƙata da aika korafe-korafe.
  • Kashi 90% na ƙwarewar dijital a makarantun firamare da sakandaren gwamnati zuwa 2031.

Tsaro Da Kula Da Muhalli

Kare Rayuka, Dukiyoyi, Hanyoyin Rayuwa Da Muhalli

Babbar Manufa

Babu tsaro ba tare da gyaran muhalli ba. Babu dorewar muhalli ba tare da tsaro ba.

Muhimman Alƙawura

  • Ƙarfafa aikin 'yan sanda a matakin jiha da al'umma, tare da sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro na tarayya.
  • Jami'an kare muhalli da masu gadin daji 1,000 daga al'ummomi, da horo da kayan aiki.
  • Gombe Goes Green: dasa bishiyoyi miliyan huɗu cikin shekaru huɗu, tare da sa ido.
  • Kammala dukkan ayyukan yaƙi da zaizayar ƙasa da ake yi, da tsarin gargaɗin wuri tare da NiMet.

Bin Diddigi

Tsarinmu Na Bin Diddigi

Ba ma neman a amince da mu ba tare da tambaya ba; muna neman yarjejeniya da aka gina a cikinta tsarin yin hisabi.

Kowane alƙawari zai zama tsarin aiki na kowace shekara, tare da hukumar da ke da alhaki, kasafin kuɗin da aka amince da shi, ma'aunin farko, matakan nasara na shekara-shekara da jadawalin sanar da jama'a, tare da tantancewa mai zaman kanta da bitar tsakiyar wa'adi.

Tsarin Nuna Matakin Ayyuka

Kowane babban aiki: wurinsa, kasafinsa, ɗan kwangila, kaso na kammalawa da hotunansa.

Rahoton Aiwatar Da Kasafin Kuɗi

Abin da aka ware a kasafi, abin da aka kashe da abin da aka cim ma.

Tsarin Bibiyar Ci Gaban Manufofi

Matsayin kowane alƙawari: Ba a Fara ba, Ana Aiki, An Kammala, ko An Samu Jinkiri.

Rahotannin Kuɗi Da Aka Tantance

Za a wallafa su a gabatar ga jama'a cikin wa'adin da doka ta tanada.

Rahoton Ra'ayoyi Da Korafe-Korafen Jama'a

Korafe-korafen da aka karɓa, aka bincika da waɗanda aka warware.

Yadda Za Mu Yi Mulki

Falsafar Gudanar Da Mulkinmu

Bin Diddigi

A kowace shekara, za mu wallafa rahoton auna ayyukanmu ga jama'a: abin da muka yi alƙawari, abin da muka aiwatar da abin da ya rage.

Ci Gaba Da Ayyukan Da Aka Fara

Za mu kare, kammala da faɗaɗa kyawawan ayyukan Gwamna Inuwa Yahaya. Ba za mu rusa abin da yake aiki ba.

Gudanar Da Kuɗaɗen Jama'a Cikin Amana

Za mu kiyaye tubalin kuɗi mai ƙarfi, hana kashe kuɗi ba bisa ƙa'ida ba, da tabbatar da cewa kowace naira tana samar wa jama'a amfani mai ɗorewa.

Tafiya Da Kowa

Ba za a bar wani mutum ko al'umma a baya ba saboda wurin zama, jinsi, ƙabila, addini ko matsayin zamantakewa.

Dr. Jamilu Isyaku Gwamna with the people of Gombe State

Domin Ingantacciyar Jihar Gombe

Alƙawarina Na Kaina

  • Zan gudanar da kuɗaɗen jama'a cikin gaskiya, yin hisabi da taka-tsantsan.
  • Zan kasance shugaba mai sauraron jama'a: zan saurari talaka da mai arziki, waɗanda suka zaɓe ni da waɗanda ba su zaɓe ni ba.
  • Zan yi mulki cikin adalci da gaskiya, in tafi da kowa ba tare da la'akari da addini, ƙabila ko jam'iyyar siyasa ba.
  • Zan yi aiki tuƙuru domin in bar Gombe cikin yanayi mafi kyau fiye da yadda na same ta.

Ku Karanta Shi. Ku Tattauna Shi. Ku Yi Tambayoyi. Ku Ba Ni Amanar Shugabanci, Ni Kuma Zan Sadaukar Da Dukkan Ƙarfina.

Jamilu Isyaku Gwamna

Sauke

Karanta Cikakken Kundin Manufofi

An rubuta shi da harshe mai sauƙi domin kowa ya fahimta, kuma an fayyace alƙawura domin kowa ya iya tantance cika su. Akwai shi da Turanci da Hausa.

Babban fayil ne. An fi so a yi amfani da Wi-Fi.

Dakta Jamilu Isyaku Gwamna

Ɗan Takarar Gwamna Na APC, Jihar Gombe

Gwamna ga Gombe

Burinsa na zama gwamna shi ne bayyanar ƙwarewarsa a fagen siyasa, wadda ya samu a harkar gudanar da kasuwanci, jagorancin cibiyoyi da ci gaban al'umma. A watan Mayu 2026, jam'iyyar All Progressives Congress ta bayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.